ABNA24 : Shugaban Majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya kuma kara da cewa; Ina taya al’ummar Iran murnar wannan gagarumar nasarar, kuma wani mataki ne da yake dakile duk wata makarkashiya da ake kitsawa Iran.
Tun kwanaki biyu da su ka gabata ne dai Iran din ta sanar da cewa za ta daga darajar Unranium din da take tacewa daga kaso 20% zuwa 60% a matsayin mayar da martani ga rashin aiki da yarjejeniyar da kasashen turai da Amurka suke yi, da kuma makarmashiyar ‘yan sahayoniya.
342/